Lalube a Duhu

Komai wataran wucewa zaiyi
Babu abu madawwami
Ko wahala ko jin dadi!
Don haka dauki rayuwa da sauki
Ka huta ma kanka tararradi

Dama duniya shi
Zuwa mukai zaman wucin gadi
Chan 'Gidan' mukewa tanadi
Muna ta kokarin yin guzuri
Kafin lokaci yayi mu tattara mu tafi

Ba wai neman 'duniya bai da amfani
Bal, kar dai ya dauke mana hankali
Mu zam tamkar 'bayi' a wurinshi
Son zuciyarmu ya zam linzami
Ya batar da mu a dokar daji

Mas'tada'a shine saiti
Dace shine a sami wadatar zuci
Ba yabo, ba fallasar asiri
Wannan shi zai kaimu ga gachi
Allah Ya tabbatar mana da alkhairi!

Haidarwali 201703241514hrs

Comments

Popular posts from this blog

A STUDY ON THE SWEETNESS OF SUGARCANE

Ramblings

A Midnight Encounter