Ina Mafita
Yawwan qorafi akan rashin daidaituwar al'umma abu ne da ya yawwaita a kafafen yadda labarai da sashe-sashe na zantawa tsakanin jamma'a.
Yawwan korafe-korafen ba shi ne abun ji ba. Hasali dai rashin samun mafita! Idan ka samu majalisu da aka hadu - ko a gidajenmu ko a waje - zaka tarar yawanci kuka kawai akeyi kuma karshe a bige da turawa 'gwamnati' ko 'shugabanni' laifi.
Toh anan sai ka rasa wai su wadannan din da aka qaqabawa laifi su waye su! Ina ce ni da kai da ke da shi da ita ne?
Shi gwamnati dai mutane ne ke hada shi sai ya zamto an rarraba muqamai. Hakanan shugabanci kuma abu ne da komai qanqantar wuri ake samu don haka yasa kaama daga iyali wanda za'a iya cewa shi ne tushen al'umma har zuwa kololuwa Shugabancin Qasa aka tanadar da tsari na shugabanci.
To meyasa nayi wannan dogon bayani? Ba wani abu ba ne illa tabbatar da cewa gyaran da muke son gani a rayuwar mu dole mu ne zamu tabbatar dashi ba wai wani chan zamu jira ya zo ya kawo mafita ba. Mu din dai mune gwamnatin, mune shuwagabannin! Don haka sai mubtashi tsaye mu fuskanci aikin da ke gaban mu.
A qarshe kuma mu sani cewa shi gyare mai dorewa baya bukatar sauri da azzarbabi amman yana son hakuri, dagewa, da bi a sannu. Don haka ne aka ce sannu-sannu bata hana zuwa, sai dai a dade ba aje ba. Amman da muguwar rawa, gwamma qin tashi. Don haka mu jure mu dage muyi hakuri don ance 'mai hakuri yakan dafa dutse, harma ya sha romonsa'!
Haidarwali 201703240001hrs
Comments
Post a Comment