Gajeren Labarin Sharholiya a Garin Injeria

Ku fa mutan Injeria kun cika son sharholiya wallahi! Yo in banda sharholiya, ina ku ina cin kayan dadi da shan leman gwangwani bayan duk duniya kowa tsuke aljihu yake yi don neman sauki dagaibtila'i na hauhawar farashi da karyewar tattalin arziki! 
.
Maimakwon a dan sami gurasa ko rogo, ko su mutan Zaria su dan yafa fate, a kora da farau-farau ko ruwan randa me dan sanyi. 
.
Toh tunda dai ba kwa son ku daidaita al'amura da kanku zamu daidaita zaman kowa! Gashi nan yanzu duk wannan nairorin du aka je aka boye sai an dawo mana da su, ma ga ta tsiya! Dama aron kudin aka bayar, zamu karbe kayanmu, in yaso duk wanda yake son sabon kudi, ya je ya yi noma! 
.
Kuma kowa ya shirya, don mun gama tsari da Majalissar dinkin Kasar Sharholiya...ai, af in nufin Kasar Injeriya za'a fito da sabon tsari shekara mai zuwa na gudanar da tattalin arziki. 
.
Babban maqasudin wannan sabon tsarin shi ne duk wanda yake son ya sha jar miya, toh kuwa sai ya yi noma ya yi girbi. An daina mana zaman banza da sharholiya da karanta wasikar jaki! Kowa dole ya zage damtse idan ba haka ba kuwa ya kwan da yunwa (dariya dara-dara). 
.
Eh mana! Ai ita yunwa ba ayi mata la haula! 
Bari dai ku gani, zamu dan tsagaita a nan ku biyo mu a shiri na gaba don jin tsare-tsaren Taswirar Yaqi da Sharholiya. 

Sanarwa: Wannan qagaggen labari ne. Idan kuka ga ya yi kama da gaske toh laifin mai karatu ne, ba bu ruwan marubuci don ba shi ne ya ke da hakkin bawa rubutu ma'ana ba. 
.
Naku a kullum, 
.
Maje Amin 202211061254hrs

Comments

Popular posts from this blog

A STUDY ON THE SWEETNESS OF SUGARCANE

Ramblings

A Midnight Encounter