Menene Tasirin Tsari ga Cimma Manufar Rayuwa?
Sau dayawa zakaga mutune suna rayuwa ne ba tare da lissafi ba. Wannan dabi'a ta samu tushe ne daga abu biyu.
Na farko shine rashin tunani akan manufar rayuwa da tunanin tsarin da za'a dora rayuwa akai. Wannan shi ke sa mutane suyi rayuwa kara-zube.
Ita kuma rayuwa, kamar yarda duk wani abu mai muhimmanci yake bukatar tsari, haka itama take bukatar ayi mata shimfida mai kyau sa'annnan a tsara yarda za'a tafii da ita wanda shi ne zai kai mutum ga gachi.
Abu na biyu kuma shi ne gurguwar fassara da ake yima 'qaddara'. Sau dayawa zaka ga babban abun da ke hana mutane su tsara rayuwarsu shi ne tunanin cewa komai a hannun Allah yake. Tabbas wannan batu haka yake babu ja. Sai dai batun kuma yanada bangaren da ake bari ba'a qarasawa.
Duk da Ubangiji Mahaliccinmu shi ke rike da komai, amman sai ya bawa mu yan Adam wani yanki na ikon zartar da harkokin rayuwarmu. Tare da wannnan ikon ne ya haliccemu da kwakwalwa wacce take ta sha banban da duk wani bangare na jiki.
Wannan baiwa ta kwakwala itace ta bawa dan Adam damar ya zama 'Khalifa' ban qasa kuma ya sarrafa duk wani nau'i ababen amfani ga rayuwarshi da ta sauran halittu.
Toh idan muka hada duk waddanan zamu gane cewa duka komai na rayuwa, Allah ya dorashi akan tsari ne na manufa. Don haka muma dole mu tabbatar mun fid da tsari a bangarorin rayuwarmu don mu cinma manufa kuma muyi nasara.
Allah ya taimakemu ya bamu ikon aikatawa ya kuma wanzar damu akan daidai.
Haidarwali 201804211050hrs
Comments
Post a Comment