Hawaye
mabubbugar yanayi
da zuciya take ciki
su ke furta yarda muke ji
a yayin da kalmomi
suka kasa bayani
wasu masu dumi da zaqi
wasu gishiri-gishiri
masu sanyaya ruhi
da masu zuba kamar an saki
da masu diga a hankali
walau ya zam na dadi
ko kuwo na juyayi
suna sace duk kalmomi
don sukan sami asali
daga zurfin zuci
baiwa daga Mabuwayi
ya bawa dan Adam shi
zuciya ta fito fili
ta bayyana yarda take ji
Iko sai Allahu Rabbi!
Haidarwali 201710052313hrs
Comments
Post a Comment