'Manyan Gobe' (Leaders of Tomorrow)
Sau dayawa zakuga ana qorafi akan matasa basa yin hobbasa wajen ganin sun gina kansu ko ta hanyar neman ingantaccen ilimi ko sana'a. Duk da cewa wannan abu haka yake, toh amman kamar yarda Hausawa suka ce: Idan bera da sata, daddawa ma da wari'.
Shi dai 'matashi' kamar yarda sunan nasa ya nuna 'tasowa' yake yi don haka dole a nusar da shi hanyar da ya kamata ya bi don samun cigaban kanshi da ta al'ummar shi.
A saboda haka ne nake ganin babban abunda matasa suke buqata a yau shi ne 'mentoring' watau 'jagoranci'. Kamar yarda makafi suke buqatar Dan-Jagora yake, haka Matasa suke buqatar 'Jagorancin Manya. Shi Babba dole ya dage ya jure yayi wa matashi 'jagora'. Da dadi, babu dadi haka za'a yi ta hakuri tunda 'yi wa wani yiwa kai ne'. Hakannan 'hannunka baya rubewa ka yanke ka yar'!
Matasa duk da matsalolin su, suna kokarin abubuwa daidai yanayin da suka sami kansu. Ya rage ga 'Jagorori' su cigaba da dagewa wajen saita su hanya har Allah ya sa su Matasan su zama manya 'GOBE'!
Haidarwali 201703260810hrs
TRANSLATION:
Many times people (Elders) complain about the falling standards of youth in pursuing knowledge and skills today. While this is undoubtedly true, we must remember that every coin has two sides. .
.
'Youth' just like the name implies, are budding, upcoming plants who are trying to find their feet and they need the nurturing and tending of the more mature and experienced to enable them grow and develop themselves - and in the process their community/society.
.
Thus, I feel the key thing that 'Youth' are in dire need of today is 'Mentoring'. Just like the case of the Blind who need a 'Sighted Guide' (or any other means as a guide), so also Youth need the guidance of Elders. Elders thus need to persevere and be patient guides to the Youth. Good or bad, through thick and thin, they must stand by them because the mentee's success, is the mentor's success and as they say: 'nothing worthwhile is ever easy'! Also, 'you do not cut your nose to spite your face'!
.
Regardless of the many issues that Youth have, they are continuously making efforts within the circumstances they find themselves and it remains the responsiblity of the Elders to continue the work of Mentoring to mould them and guide them to fulfill their potential as Leaders of Tomorrow!
.
Haidarwali 201703260850hrs
Comments
Post a Comment