Masu Gida da Iyalansu





Ka shi na Farko

Tanko: Salamu Alaikum (Ana gyara da babbar murya). Ina kike, maza kowa mun abinci inci zanje majalisa.
Ladidi: Wa alaika Salam, toh Maigida baza ka dan huta ba.

Tanko: Wane hutu, so kike in kunshe a daki kamar marar lafiya.
Ladidi: A'a wai ka shawo aiki tun safe kuma da sai ka dan huta ba muyi hira.

Tanko: Hira! Hirar me zamuyi banda kiyi mun tsegumi da gulma. Ke ba fita kike ba bare ki san abun da duniya take ciki. Dan Allah yi maza kar labari ya wuce ni!
Ladidi: Allah ya baka hakuri (Ta kawo abinci da ruwan sha ta ajiye to kome gefe guda ta zauna).

Tanko: (Ya bude kwanon abinci ya fara zubawa) Ke kuwa Ladidi ba kya jin magana ta na ce bana son zumbutun kazan nan amma sai da kika sa min a abinci (murtuke fuska da fushi).
Ladidi: Yi hakuri maigida mantawa nayi ban cire ba ina sauri, ka kusan dawowa ban idda girki ba. Bara inje in gyaro maka shi, kasan tsokar tafi yawa ta nan bangaren ne.

Tanko: Kyale kawai zan cire. A dai lura dan gaba. Gashi gishiri ma duk yayi yawa. Ba kya dandana abincin ne idan kina dafawa?
Ladidi: Ayya, kayi hakuri.

A WANI GIDAN KUMA

Iro: Yar Malam sannu da kokari, Kai! Na barku tun safe ku kadai ko?
Yar Malam: A'a babu komai ai nema sai an fita.

Iro: To me kika samu kiyi da bana nan (yana murmushi).
Yar Malam: (Ita kuma dariya ya kamata ta kyalkyala): Kawai na dan yi wanki ne nayi daka don dama fura ta kare nake son in sami wacce zan dama maka. Yanzun nan ma na gama dama maka don yaron da ya fita ma shi ya siyo kankarar da na dama da shi.

Iro: Kai! (Yana tande baki) Yar Aljanna ke nan! Duk ke kadai kika zuba wannan aikin, agaisheki. A wannan ma ku mata kuna kwashe lada ne kawai.
Yar Malam: Toh Allah ya hada mu a ladan. Ga furar nan ka fara da ita bari inje in kawo abincin kuma ina da labari.

Iro: Toh Madalla, Allah yayi miki albarka. Jeki ki dawo ki ban labarin nan kinga ai babu abbun da zai sani in fita sai gobe, zan huta kawai abina.
Yar Malam: Lallai maigida furar ta kawo haske!

Iro: Zancen kike so ance da gwauro ya iyali! Malam Tanko ma sai dai ya tafi majalisa shi kadai don kuwa yau ni faashin zuwa zanyi. Toh menene labarin, kinsan ni ina jin dadin sautin muryarki idan muna hira.
Yar Malam: Hakane ko. Kace zan fara chazar ka kudi kenan...

Zamu dora nan gaba Insha-Allah.

Maje Amin 201401061500hrs

Comments

Popular posts from this blog

A STUDY ON THE SWEETNESS OF SUGARCANE

Ramblings

A Midnight Encounter