Tsakanin Burin Zuciya da Amanar Al'umma

Da ace zaɓi yana hannuna, da rayuwata ba zata kasance mai hayaniya ba.

Da zan yi iya ƙoƙarina wajen sauke amanar da ke kaina, na taimaki mutane gwargwadon ikon da Allah Ya ba ni, sannan na koma na zauna a garinmu. Zan dan sami karamin lambu mai shuke-shuke,🌱 ina kula da ƙananan kifaye a bayan gidana. Da safe da maraice in fito in watsa musu abinci, ina kallonsu suna shawagi cikin ruwa mai garai-garai ina shauki da ni-imar Allah Subhana Azzawajalla! Can kuma da yamma mutum ya sami ƙarƙashin wata inuwa da dan wani 🍹lamurje mai sanyi a gefe,☺️ ana hira da mutanen gida ko abokan arziki cikin annashuwa. Wani lokaci a yi karatu📚, wani lokaci ayi lazimi📿, wani lokaci kuma a yi shiru, a yi tafakkari da godiya ga Allah bisa ni'imominSa.

Don sau da dama mutum baya bukatar hayaniya, mulki ko neman ɗaukaka. Idan so samu ne, kawai mutum ya rayu lafiya da mutane, ya yi iya kokarin abin da Allah Ya ɗora mai, sannan ya jira ranar da Allah Zai ce lokaci ya yi, ya tattara kayanshi ya koma gare Shi, Madaukaki.

_Amma kash!_ Rayuwa ba haka take ba, don ba kasafai mutum yakan sami abin da yake so ba! Wani lokaci, abin da zuciya take marmari yakan saɓa da abin da amanar da Allah Ya ɗora wa mutum take buƙata.

Don kuwa idan Allah Ya albarkaci mutum da ilimi, basira, hangen nesa ko damar yin tasiri ga rayuwar al'umma, sau da yawa ba ya samun damar zaɓar rayuwar natsuwar da yake buri. Dole ya shiga cikin wuraren da bai taɓa fatan shiga ba. Dole ya fuskanci rigingimu, sabanin ra'ayi, suka, zargi da ƙalubale. Wani lokaci har ya shiga harkokin da, da ace zaɓi yana hannunsa, da ya fi son ya nisance su.

Abin takaici kuma shi ne, in dai akace mutanene zasu yi mu'amala, toh ba za a rasa rashin fahimta, rikici, ko ma zalunci ba. Mutum zai iya shiga haƙƙin wani ba tare da ya yi niyya ba. Zai yi abubuwan da zasu jawo masa baƙin jini ko ya iya zama sanadin ƙirƙiro masa gaba saboda kawai ya tsaya kan abin da ya yi imani shi ne daidai.

Toh tambayar anan shine, idan duk masu ilimi, masu kishin ƙasa da masu hangen nesa suka zaɓi rayuwar natsuwa irin wace na bayyana a sama, suka janye daga hidimar jama'a, wa zai tsaya ya ɗauki wannan nauyi?

Wataƙila wannan shi ne babban darasin rayuwa.

Ba kowa ne Allah Ya halitta zai rayu yadda zuciyarsa take so ba. Wasu an ƙaddara musu su sadaukar da wani ɓangare na jin daɗinsu domin wasu su sami rayuwa mafi kyau. Shi ya sa nake ganin cewa dole mu gane cewa rayuwa ba ta mutum kaɗai ba ce. Muna da hakki a kan al'ummarmu. Muna da abin da ya kamata mu bari a matsayin gudummawa ga waɗanda za su zo bayanmu. Duk wani ilimi, gogewa, ko hikimar da Allah Ya ba mu, ba mallakarmu ba ce. Amana ce.

Saboda haka, idan Allah Ya ƙaddara cewa sai mun ɗan jinkirtako ma hakura da rayuwar natsuwar da muke mafarki da ita domin yi wa al'umma hidima, to sai mu roƙi Allah Ya ba mu ikon yin hakan da adalci, da ikhlasi, da tsoronSa.

Kuma idan wannan sadaukarwa ta kasance saboda Allah kaɗai, ba don yabo ba, ba don mulki ba, ba don tarihin duniya ba, to muna fata ta zama sanadin gafarar kurakuramu.

Allah Ya karɓi ɗan abin da dukkanmu muke kokarin dabbakawa da ikhlasi, Ya yafe abin da muka kasa yi, Ya kuma ba mu babban rabo a ranar da dukiya, matsayi, ko suna baza su amfanar ba, sai dai kawai aikin ƙwarai. Don a ƙarshe, ba abin da muka tara ba ne zai bi mu ko yabon mutane ne zai tsaya mana ba. Abin da zai rage a ranar gobe kiyama shi ne yadda muka cika amanar da Allah Ya ɗora mana.

Allah Ya sa idan lokacin tafiyarmu ya yi, mu tattara kayanmu cikin natsuwa, mu koma gare Shi tare da yardarSa da rahamarSa. *Amin.*

Haidarwali 202607161603hrs

Comments

Popular posts from this blog

A Midnight Encounter

Open Letter to Members of NASS

My Perception of Life…