Rubutu A Harshen Asali
Rubutu a harshen asali - ba Hausa kawai ba - abu ne mai matukar muhimmanci don ta harshe ne ake yadda al'ada. Shi yasa yawan amfani da yaren aro kamar Turanci zai iya zama tarnaki wajen sadar da asalin 'madara' da 'romon' al'adunmu na gargajiya. Idan abun yayi zurfi ma sai ta kai ga masu amfani da 'yaren aro' sun zama suna kwaikwayon halayya da al'adun mutanen da suka aro 'harshen'. Irin haka ke sa a fara kiran mutum sunaye kamar 'baqin balarabe' ko kuma 'baqin bature'!
Ko da yake tasirin yaren Turanci zai iya sa mutum kwaikwayon dabi'u masu kyau kamar riqe alkawari da amana wanda abu ne da za'ayi murna dashi. Sai dai sau da yawa wasu abubuwan ake kwaikwaya basa dacewa da yanayin mu. Irin haka ke sa kaga mutum ya zama tamkar jemage - baka ga tsuntsu, baka ga dabba!
Yin rubuta da harshen Hausa yana daga cikin babban abun da ya sa harshen Hausa ya bunqasa ya kuma qara qarfafuwa musamman dayake anyi amfani da shi wajen sadar da ilimin fannuka dabban daban a yayin da aka kirkiro rubutun Ajami - rubutacciyar Hausa da harrufan larabci. Wannan shima ya bada gudummawa wajen ganin Hausawa sun dabbaqa wasu al'adu na mutanen Larabawa. Watakila kuma zuwan Turawa da suka kawo nasu yaren sa'annan suka musanya harufan rubutu ya koma na Latinanci ya dan kawo nasa tasirin wajen shigar da wasu kadan daga cikin dabi'u da halayyar zamantakewar Turawa cikin al'adun Hausawa. Sai dai daga dukkan alamu wannan tasirin bai karfin ba don ganin cewar har yanzu al'adun Hausa sunfi kusanci da na larabawa saboda daddewar da akayi wajen mu'amala da kuma kyakyawan zamantakewa da ke tsakanin Larabawan da Hausawan.
A karshe ko wane yarene muka dauka aka dauka zamu ga cewa rubutu yana matukar tasiri wajen dabbaqa da wanzar da al'adun mutanen da suke amfani da yaren. Don haka ne nake goyon bayan duk wani yinkuri na ganin anyi amfani da harsunanmu na asali wajen rubuce-rubuce don shi ne zai tabbatar da cigaba da yada kyawawan al'adunmu na gargajiya. Kuma a kullum nakan fadawa mutane cewa ko da da wani yaren mutum zaiyi rubutu, toh ya tabbatar yayi 'tunani a yarenshi' yarda a yayin da yake rubutun zai sadar da madara da romon al'adarsa wanda shine yake tabbatar da tushe da kuma asali.
Haza wassalam.
Haidar Wali 201701311030hrs
Comments
Post a Comment